Kwamitin Tsaro ya saka takunkumi a kan IS

ISIS Hakkin mallakar hoto AFP

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kudiri da ke da nufin dakile hanyoyin samun kudaden shiga daga fasakwaurin mai, da sayar da tsaffin kayayyakin tarihi da kuma biyan kudin fansa ga masu da'awar jihadin kasar Musulunci.

Mayakan kungiyar IS masu da'awar kafa kasar musulunci a Syria da Iraki suna samun makudan kudade daga haramtattun ayyuka na sayar da danyen mai da kayan tarihi ta hannun wasu dillalai.

Kudirin na barazanar sanya takunkumi kan duk wanda ya sayi mai daga kungiyar ta IS da kuma haramta safarar kayayyakin sarrafa man.

Wani wakilin BBC a Majalisar Dinkin Duniya ya ce amincewa da kudirin ya nuna yadda kasashen duniya suka hada kansu don yakar mayakan na IS.