'Yan Boko Haram sun kashe mutane 21 a Borno

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kasashen Najeriya da Kamaru da Chadi da kuma Nijar na hada dakarun hadin gwiwa domin yakar Boko Haram

Wasu mutane da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun hallaka mutane akalla 21 a wasu hare-haren da suka kai kauyen Akida da Ladin Mbuta da jihar Borno.

Maharan sun kashe 12 a kauyen Akida, yayin da suka hallaka wasu mutane tara a kauyen Ladin Mbuta a karamar hukumar jere da ke jihar ta Borno a Najeriya.

Kauyukan biyu dai na da tazarar kusan kilomita 20 ne zuwa 25 daga Maiduguri babban birnin jihar.

Yawancin wadanda 'yan Boko Haram din suka kashe a garin Ladin Mbuta tsofaffi ne kamar yadda wani ya shaida wa BBC.

Kuma sai da mayakan suka daure hannayensu sannan suka rika harbinsu, haka kuma sun yanka wasu.

A ranar Alhamis ne dai wata 'yan kunar bakin wake ta kashe mutane shida, yayin da aka kama wasu mata biyu kafin su tayar da bama-baman da ke jikinsu a garin Biu na jihar ta Borno.