'Ba mu da halin daukar nauyin 'yan gudun hijira'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kafa dokar ta-baci a jihar Diffa don yaki na Boko Haram

Hukumomin Damagaram a Nijar, sun ce ba su da karfin daukar dawainiyar 'yan gudun hijira sama da 4,700 da suka gudo daga Diffa saboda rikicin Boko Haram.

Gwaman Damagaram, Kalla Muntari ya yi kira ga masu gudun hijirar da su je gidajen 'yan uwansu ko su san yadda zasu yi.

Inda ya kara da cewa gwamnatin jihar ba ta da niyyar bude sansanin 'yan gudun hijira wadanda yawancinsu mata ne da kananan yara.

A halin yanzu ana samun 'yan gudun hijira kusan 50 a gidan mutum guda.

Hakan na zuwa ne yayin da kawancen jam'iyun adawa na ARDR ya zargi shugaban kasar Alhaji Mahamadu Issoufou da jefa kasar cikin rikicin Boko Haram.

Yayin da kuma suka bukaci a bai wa sojojin kasar isassun kayan aiki domin tunkarar kalubalen.

Sai dai jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki ta yi watsi da zarge-zagen 'yan adawan tana mai cewa lamarin boko haram akida ce da ta zamanto ruwan dare gama duniya.