An soki Obama bisa kisan musulman Amurka

Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption An soki Obama saboda rashin yin cewa komai bisa kisan musulmai

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya soki shugaba Obama na Amurka saboda rashin cewa komai game da kisan da aka yi wa wasu matasa musulmi su uku a North Carolina.

Mr Erdogan ya ce idan har 'yan siyasa suka yi gum da bakinsu a irin wannan yanayi, to duniya ma ba za ta taya su jaje ba idan aka kashe mutanensu.

Tunda farko, mahaifin daya daga cikin mutanen uku da aka harbe har lahira a lardin Chapel Hill ya fadawa masu makoki a wajen jana'iza cewa kisan wani laifi ne na kiyayya.

An kashe daliban uku ne ranar Talata.

Daliban dai su ne Deah Shaddy Barakat da matarsa, Yusor Mohammad Abu-Salha, mai shekaru 21, da kuma kanwarta, Razan Mohammad Abu-Salha, mai shekaru19.

An kama wani mutum mai suna Craig Stephen Hicks, dan shekaru 46, bisa zargin kisan nasu.

An zargi kafafen watsa labarai da kin jinin musulmai

Da farko dai ba a bai wa labarin muhimmanci ba, har ma 'yan sandan garin suka fitar da sanarwar da ke cewa kisan ya faru ne bayan daliban sun samu rashin jituwa da wanda ake zargi ya kashe su a kan wajen da kowanne zai ajiye motarsa.

Sai dai mahafin Abu-Salha ya musanta wannan zargi, yana mai cewa an yi kisan ne "saboda tsanar da ake yi musu".

Masu fafutika a shafukan intanet sun soki manyan kafafen watsa labaran duniya saboda rashin bai wa batun muhimmanci.

Hakan ne ma ya sa suka kirkiro da wani take mai suna #ChapelHillShooting domin janyo hankalin duniya kan batun, kuma ya zuwa yanzu fiye da mutane 900,000 sun yi amfani da shi.

Hasalima, wannan take shi ne ya fi jan hankulan mutane a Amurka da Burtaniya da Masar da Saudi Arabia da kuma kasashen Gabas ta Tsakiya da dama.

Yawancin wadanda ke amfani da wannan take sun zargi manyan kafafen watsa labarai da cewa ba sa yi wa musulmai adalci, suna masu cewa da a ce musulmi ne ya yi kisan da tuni "an bayyana shi a matsayin dan ta'adda".