Olukolade ya maida wa Niger martani

Hakkin mallakar hoto
Image caption Majalisar dokokin Niger ta amince a tura sojojin kasar zuwa Nigeria

Kakakin rundunar sojan Najeriya Manjo janar Chris Olukolade,ya ce ko kadan rundunar sojan Najeriyar ba ta ji dadin kalaman da Ministan tsaron Niger ya yi ba, inda ya ce sojojin Najeriyar matsorata ne kuma suna tserewa 'yan Boko Haram a filin daga.

Janar Olukolade ya yi amfani da shafinsa na twitter domin mayarwa da ministan tsaron Niger din martani game da wadannan kalamai

Ya ce sojojin Najeriya sun kware akan aikinsu kuma su na daraja sojojin kasashe makwabtansu

Manjo Janar Olukolade ya bayyana cewa sojojin na Najeriyar su na da jarunta da kuma kishin kasa, duk kuwa da irin zagi da kuma zargin da suke fuskanta a ciki da kuma wajen kasar.

Ya kara da cewa ba za su amince wata kasa ta rika bayyana sojojin Najeriya a matsayin matsorata ba.

Olukolade ya ce irin wannan mummunan zargi ba shi da wata manufa illa batawa sojojin Najeriyar suna.

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai bayan majalisar dokokin Nijar din ta amince gwamnati ta tura sojojinta domin yaki da Boko Haram, ministan tsaron Nijar din Mahammadu Karijo ya yi wadannan kalamai

Duk kokarin da BBC ta yi na samun minista Muhammadu Karijon don jin ko zai baiwa sojojin Najeriyar hakuri ya ci tura