Ebola: Ana kai wa ma'aikatan agaji hari a Guinea

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A bara an kashe wasu ma'aikatan agaji takwas a kasar ta Guinea

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce ma'aikatan agaji na fuskantar barazana a fafutukar da suke na yaki da cutar Ebola a kasar Guinea.

Inda ta ce akalla ana kai wa ma'aikatan agaji hari sau goma a duk wata.

Harin baya-bayan nan ya auku ne a ranar Lahadi, inda wasu mutane suka yi wa wasu ma'aikatan sa kai biyu na kungiyar duka, a yayin da suke kokarin binne wata gawa.

A wata sanarwa da shugaban Red Cross a Guinea ya fitar, Youssouf Troare, ya ce ba za a iya dakatar da cutar Ebola ba har sai mutane sun sauya tunaninsu a kasar.

Inda ya kara da cewa ba za su lamunci yadda ake yiwa ma'aikatan agaji ba.

Lamarin na zuwa ne a yayin da Amurka ke shirin janye dakarunta daka Liberia, wadanda aka tura domin yaki da cutar ta Ebola.

Kasar dai ta tura dakaru 2,800 Afrika ta Yamma ne a lokacin da cutar ta yi kamari, amma ta janye 1,500 daga yankin.

Ko da yake Mr. Obama ya ce fararen hula 10,000 za su ci gaba da taimaka wa wajen kawo karshen cutar a Yammacin Afrikan.