Google zai fara ba da bayanan kiwon lafiya

Hakkin mallakar hoto GOOGLE
Image caption Hajar za ta rika bayar da bayanan alamun cututtuka da maganinsu

Shafin intanet na Google zai bullo da wata haja da za ta rika bai wa mutane bayanan kiwon lafiya a kan wasu sanannun cututtuka.

Hajar za ta rika bayar da bayanai a game da alamun cututtuka da hanyoyin magance su.

Kanfanin Google ya ce yana aiki tare da wasu likitoci domin samar da hajar, amma ya ce hajar ba tana nufin maye gurbin ziyartan kwararrun likitoci bane.

Hajar idan aka samar da ita za ta fara aiki ne a Amurka.

Kamfanin Google ya ce ya kuduri aniyar ganin ana amfani da hajar a ko ina a duniya nan gaba, tare kuma da kara wasu cututtuka da ba sanannu ba.

Likitoci a Burtaniya sun yi marhabin da yunkurin na Google, sai dai sun yi gargadin cewa akwai bukatar a rka tantance bayanan kafin su yi wa jama'a daidai.

Wannan yunkuri shi ne na baya bayannan da kamfanin Google ya yi na shiga sha'anin kiwon lafiya gadan gadan.

A bara kamfanin ya sanar da cewa yana daukar nauyin bullo da wata haja ta gano cutar sankara da bugun zuciya.