'Yan bindiga sun kai hari jahar Gombe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram

Rahotanni daga jihar Gombe dake arewa maso gabashin Nijeriya na cewa hukumomin jihar sun kafa dokar hana fita ba dare ba rana, a cikin birnin Gombe.

Wannan ya biyo bayan farmakin da wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai a cikin birnin da ma wasu garuruwa a jihar.

Mazauna jihar dai sun ce mayakan sun rarraba wasu takardu masu dauke da wasu sakwanni game da zabukan da ake shirin yi a Nijeriya.

Wasu bayanai na cewa mayakan sun farwa jami'an tsaro, kafin daga bisani suka fice, kuma an gansu akan hanyarsu ta zuwa jihar Borno.