Ukraine: An fara aiki da yarjejeniyar tsagaita

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Da tsakiyar daren Asabar ne yarjejeniyar ta fara aiki

An fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin sojojin gwamnatin Ukraine da 'yan tawaye da ke samun goyon bayan Rasha a gabashin Ukraine.

Rahotannin sun ce bangarorin biyu da basa gamaciji da juna sun dakatar da lugudan wuta yayin da yarjejeniyar ta fara aiki a tsakiyar daren Asabar.

Gabanin fara aiki da yarjejeniyar, bangarorin biyu sun zargi juna da neman bata ta.

Shugaba Petro Poroshenko ya ce sojojin Ukraine ba za su yi kuskuren juya dayan kunci a daka ba, idan 'yan tawayen suka mare su a dayan gefen.

Jami'ai a Ukraine sun ce fiye da mutane 5400 aka kashe tunda aka fara dauki ba dadin a gabashin Ukraine a watan Afrilun bara bayan Rasha ta mamaye yankin Cremea.