Bam ya fashe a Damaturu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bam ya fashe a Damaturi

Rahotanni daga Damaturu,babban birnin jihar Yobe a arewacin Najeriya na cewa wani bam ya fashe a wata tashar mota, a birnin, ranar Lahadi.

Duk da cewa ba bu takamaiman yadda al'amarin ya faru,amma shaidu sun tabbatar da cewa akalla mutane takwas ne suka rasa rayukansu sannan wasu da dama sun jikkata.

Kawo yanzu dai ba bu wani mutum ko kungiya da ya dauki alhakin kai harin.

Wannan na faruwa ne kwana daya bayan harin da wadanda ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a jihar Gombe da kuma wani yunkurin 'yan bindiga a garin Kibiya ta jihar Kano.

Jihar Yobe dai na daya daga cikin jihohi ukun da 'yan kungiyar Boko Haram suke kai wa hare-hare, a arewa maso gabashin Najeriya.