Bam ya kashe mutane 8 a Damaturu

Hakkin mallakar hoto EPA

A Najeriya wata 'yar kunar bakin wake ta tayar da bam a garin Damaturu ta kashe akalla mutane bakwai.

Rahotanni daga Damaturun, babban birnin jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriyar, sun ce 'yar kunar bakin waken ta tayar a bam din ne a babbar tashar motar garin.

Mazauna birnin sun ce tashin bam din ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane takwas, yayin da sama da talatin kuma suka samu raunuka.

Hakan dai ya faruwa ne kwana daya bayan harin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a jihar Gombe da kuma wani yunkurin da wasu 'yan bindiga suka yi na kai hari a garin Kibiya ta jihar Kano.

Jihar Yobe dai na daya daga cikin jihohin da 'yan kungiyar Boko Haram ke kai wa hare-hare a arewacin Najeriya.

Karin bayani