An fara zaman makoki na kwanaki 7 a Masar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mayakan IS sun kashe kiristocin Masar 21

Shugaban kasar Masar, Abdel Fattah El Sisi ya sanar da zaman makoki na kwanaki 7 a kasar saboda kashe kiristocin kasar 21 da kungiyar IS ta yi a Libya.

Wani hoton bidiyo da aka fitar, ya nuna yadda mayakan kungiyar ta IS suka fiffile kawunan mutanen da suke garkuwa da su, wadanda suka kama a birnin Sirte a watannin Disamba dana Janairu.

Kiristocin sun yi balaguro zuwa Libya ne domin samun aikin yi.

Shugaba Abdel Fattah El Sisi ya kira taron majalisar tsaron kasar domin tattauna irin matakin da zasu dauka.

Dubban 'yan kasar Masar ne suka ketara iyakar kasar zuwa Libya domin neman aikin yi, duk da cewa gwamnatin Masar din tana horan su da su dai na yin balaguron.