Buhari na yakin neman zabe a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Buhari ya ce zai tabbatar da tsaro idan aka zabe shi

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari, yana jihar Borno domin gudanar da gangamin yakin neman zabe ranar Litinin.

Bayanai sun ce Buhari da 'yan tawagarsa suna Maiduguri ne domin zawarcin masu kada kuri'a duk da cewa ana fama da rashin tsaro a fadin jihar.

Rahotanni na cewa dubban mutane ne suka tarbe shi a birnin na Maiduguri.

Da ma dai Janar Buhari ya ce wanzar da tsaro na daga manyan batutuwan da zai bai wa muhimmanci idan ya ci zabe.

Jonathan ma ya je Maiduguri

A nata bangaren, gwamnatin jihar Borno ta ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutun aiki domin yi wa Janar Buhari maraba da zuwa.

Shi ma dan takarar jam'iyyar PDP, Shugaba Goodluck Jonathan tun a cikin watan Janairu ya kai ziyara a jihar Borno inda ya bukaci al'ummar yankin su kara ba shi dama domin tabbatar da zaman lafiya a cikin jihar da kuma yankin arewa maso gabashin Nigeria.

Jihar Borno ce wurin da aka soma rikicin Boko Haram, kuma hare-haren kungiyar sun raba mutane fiye da miliyan uku da muhallansu.

A halin yanzu dai akwai kananan hukumomi kusan 14 a Nigeria da ke karkashin ikon kungiyar Boko Haram.