Wasu shugabannin Afirka na taro a Yaounde

Sojojin kasar Chadi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin kasar Chadi

Wasu daga cikin shugabannin kasashen Afrika na wani taro a Kamaru don tattauna yadda za a kawo karshen ayyukan kungiyar Boho Haram.

Shugabannin kasashe shida ne su ka samu halartar taron a Yaounde, babban birnin Kamaru.

A farkon watan nan ne Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar da kuma jamhuriyar Benin, su ka amince da samar da rundunar hadin gwiwa ta yankin don yaki da masu tada kayar bayan.

Sai dai har yanzu akwai batutuwan da ba a gama shawo kansu ba kamar samar da kudade.

Al'amuran kungiyar Boko Haram dai na cigaba da karuwa a sauran kasashe da ke makwabtaka da Najeriyar.