Masar ta kai wa kungiyar IS hari a Libya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masar ta yi amfani da jirage samfarin F16

Masar ta ce ta jefa bama bamai a kan masu ikirarin Jihadi a makwabciyarta kasar Libya.

Matakin na zuwa ne bayan 'yan gwagwarmaya a Libya da ke da alaka da kungiyar IS suka kashe wani gungun Kiristoci kibdawa na Masar.

Sojin Masar sun ce jiragen yakin shida samfarin F16 sun hari sansanonin kungiyar ta IS da wuraren horaswa da kuma yankunan adana makamai a wani harin jiragen sama da suka kai da asubahi.

Kakakin Firayi Ministan Libya, Mohamed Azazza, ya ce an kai hare-haren saman guda takwas a garin Derna ne wanda ke karkashin ikon ma su ta da kayar bayan, da hadin kan gwamnatin Libya.

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi, ya sha alwashin daukar fansa bayan da aka nuna wani bidiyo a ranar Lahadi, da ke nuna yadda aka fille kan kirstoci kibdawan.