Mutane sama da 34 sun mutu a harin bam a Biu

motocin yaki Hakkin mallakar hoto AP

Rahotanni daga garin Biu na jihar Borno a Najeriya na cewa wani abu da ake zaton bam ne ya tashi a garin da safiyar ranar Talata.

Bayanai dai sun nuna cewa bam din ya fashe ne a wani wajen binciken ababen hawa a kan hanyar Maiduguri zuwa Miringa.

An ambaci wasu majiyoyin asibiti a garin na Biu suna cewa mutane sama da 34 ne suka mutu.

Akwai kuma wasu mutanen sama da shirin da suka jikkata.

Garin na Biu dai ya fuskanci hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram a baya.