Boko Haram ta kai hari a kan Askira Uba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan Boko Haram sun kashe dubban mutane tun daga shekarar 2009

Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari kan garin Askira Uba na jihar Borno da ke arewacin Najeriya.

Mazauna garin sun shada wa BBC cewa 'yan Boko Haram din sun fara kai hari ne ranar Lahadi da yamma, kuma sun kona gidan sarkin garin.

A cewarsu, 'yan kungiyar ta Boko Haram sun koma garin ranar Litinin, suka kona baki daya garin.

Sun kara da cewa dukkan mutanen garin sun gudu, koda yake akwai tsofaffi da suka rage, wadanda ba za su iya ficewa daga garin ba.

Wani makusancin sarkin garin ya gaya wa BBC cewa sun sanar da hukumomi batun tun kafin akai harin amma ba a dauki mataki ba.

Wannan lamari na faruwa ne kwanaki kadan bayan rundunar sojin kasar ta ce ta kwato garuruwan Monguno da Marte daga hannun 'yan kungiyar ta Boko Haram.