Masar ta bukaci taimakon kasashen duniya

Shugaban Masar Abdul-Fata al-Sisi
Image caption Masar na bukatar kasashen duniya su taimaka dan kawo karshen ayyukan mayakan IS.

Masar ta bukaci taimakon kasashen duniya domin su mara mata baya wajen yakar mayakan kasar Musulunci na kungiyar IS a kasar Libya.

Kiran na zuwa ne bayan jiragen yakin Masar din marasa matuka sun kai barin bama-bamai a sansanonin masu tada kayar bayan, a matsayin martani ga kisan da aka yiwa wasu mabiya addinin Kirista 'yan kasar da ke zaune a Libya.

Jakadan Masar a Burtaniya Nasser Kamel, ya shaidawa BBC cewa kwale-kwale makare da masu tada kayar baya ka iya isa tarayyar turai cikin makwanni masu zuwa matukar ba a dauki mataki akan hakan ba.

Kasar Italia ta ce za ta fi amincewa da jagorancin sojojin Majalisar Dinkin Duniya su wanzar da zaman lafiya a Libya, sai dai ta amince da duk wani hadin gwiwa da za a yi na gaggawa.

Hare-haren da kungiyar tsaro ta NATO ta kai a kasar Libya, shi ya yi sanadiyyar hambarar da gwamnatin Conel Muhammad Ghaddafi a shekarar 2011, sai dai tun daga lokacin kasar ta shiga tsaka mai wuya ta fuskar rashin zaman lafiya.