Jonathan na son nada sabbin ministoci takwas

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mr Jonathan na shirin fuskantar zabe a watan Maris

Shugaba Najeriya, Goodluck Jonathan, ya mika sunayen mutane takwas da yake son nadawa ministoci ga majalisar dattawan kasar.

A wata wasika da shugaban majalisar dattijai, David Mark, ya karanta a zauren majalisar, ya ce Mr Jonathan na son nada wasu sababbin ministoci ne domin maye gurbinsu da wadanda suka yi murabus.

Mutane takwas din su ne: Patricia Akwashiki (Nasarawa), Augustine Akobundu (Abia), Fidelis Nwankwo (Ebonyi), Hauwa'u Lawan (Jigawa), Musiliu Obanikoro (Lagos), Kenneth Kobani (Rivers) da kuma Joel Danlami Ikenya (Taraba).

A cikin watan Oktoban bara ne wasu ministoci suka yi murabus domin shiga takara a zabukan kasar.

A ranar Talata ne majalisun dokokin kasar suka koma zama bayan hutun da suka yi domin gudanar da yakin neman zabe.