2015: Za mu hana zabe a Nigeria- Shekau

Shekau,Jagoran Boko Haram Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shekau,Jagoran Boko Haram

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya lashi takobin hana gudanar da babban zaben Nijeriya da ake shirin yi a watan gobe.

Ya yi wannan barazana ce a wani sabon faifan bidiyo da ya wallafa ta shafin Twitter.

Akalla mutane arba'in ne suka mutu a wannan makon sakamakon hare-haren kungiyar ta Boko Haram.

Rahotanni sun bayyana cewa ana ci gaba da gwabza fada a arewa maso gabashin kasar kusa da birnin Maiduguri, tsakanin 'yan Boko Haram da dakarun soji kusa da iyakar kasar da Chadi.

Karin bayani