'Yan tawayen Ukraine sun kwace tashar jirgi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikicin Ukraine ya yi ya lafa

'Yan aware da Rasha ke goyon baya a gabashin Ukraine sun ce sun kwace iko da tashar jiragen kasa da ke wajen garin Debaltseve.

Ana dai ci gaba da gumurzu a babbar tashar sufurin, wacce ke tsakanin garuruwan Donetsk da Luhansk da ke karkashin ikon 'yan awaren, duk kuwa da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a makon jiya a birnin Minsk.

Hukumar tsaro ta turai ta ce tana magana da sojojin Ukraine da na Rasha daga cibiyar hadin kai da ke yankin.

Kakakin hukumar OECE,Michael Bociurkiw ya ce "a yankin Luhansk 'yan awaren sun ce sun fara janye tankokin yaki da makaman artilari su daga bakin daga."