Shin Boko Haram na da alaka da kungiyar IS ?

Hakkin mallakar hoto Boko Haram Twitter
Image caption Shekau a sabon bidiyonsa da yake barazana kan zaben Nigeria

A cikin 'yan watannin da suka wuce, kungiyar Boko Haram na amfani da shafin Twitter da ake rubuta da larabci domin wallafa bidiyo da hotunan hare-haren da mayakanta ke kai wa.

Amfani da shafukan zumunta da kuma intanet wata alama ce da ke nuna alakar Boko Haram da kuma kungiyar IS mai ikirarin jihadi a kasashen larabawa.

Yadda ake rubutu a shafin twitter din ya yi kama da irin wanda 'yan kungiyar IS ke yi, watau rubutan da bai wuce layi daya ba, wanda ke nuna hare-haren Boko Haram.

A baya Boko Haram na fitar da bidiyo ne a faifan DVD ko CD inda shugabantan ke magana da harshen Hausa da Kanuri da kuma Larabci, amma a yanzu bidiyon kungiyar na kunshe da rubutun da aka fassara da harshen Ingilishi da kuma Larabci.

'Sabon Bidiyo'

Daya daga cikin bidiyon na nuna yadda wani dan Boko Haram ke kokarin wayar da kan jama'a a kan ayyukan kungiyar.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban kungiyar IS, alBaghadadi

An dakatar da shafin Twitter na kungiyar na farko da ta bude a cikin makonni biyu.

Shafinta na biyu an wallafa bidiyon shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, yana barazanar hana yin zabukan da ke tafe a Nigeria.

Shekau ya dade yana mubaya'a ga kungiyar IS amma har yanzu kungiyar IS ba ta ce komai ba game da kungiyar Boko Haram.

Kungiyar Boko Haram dai ta yi ikirarin kafa daular Musulunci wadda ke da shalkwata a garin Gwoza na jihar Borno.

Wata mujallar kungiyar IS da aka wallafa a kwanan nan ta ce akwai masu jihadi a Nigeria da suka yi ma kungiyar mubaya'a amma babu tabbas ko kungiyar Boko Haram ce.