An sasanta da 'yan tawaye a Mali

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Mali Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Mali

Gwamnatin kasar Mali ta amince da yarjejeniyar dakatar da kai duk wasu hare-hare kan juna da Kungiyoyin 'yan tawaye da Abzinawa ke jagoranta a arewacin kasar.

Yarjejeniyar wani yunkuri ne na baya-bayan nan na sasantawa tsakanin bangarorin biyu da Majailsar Dinkin Duniya ke daukar nauyi.

Kungiyoyin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sun hada da ta MNLA da ta larabawa Azawad.

Sai dai masu aiko da rahotanni sun ce har yanzu akwai batutuwan da ba a cimma matsaya a kansu ba da suka shafi yadda za a raba mukamai a yankin sahara dake arewacin kasar wanda 'yan tawaye ke kira Azawad.

Karin bayani