Thailand ta haramta zama iyayen sojan gona

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasar indiya ma ta shahara kan sana'ar mata iyaye sojan gona

Majalisar dokokin kasar Thailand ta haramta wa matan kasar zama iyayen sojan gona ga ma'aurata 'yan kasashen waje.

Ma'aurata 'yan kasashen waje dai na biyan mata a kasar kudade domin su dauki ciki su kuma haifa musu 'ya'ya.

A yanzu majalisar ta ce matan kasar za su iya zama iyayen sojan gona ne kadai ga ma'auratan da akalla daya daga cikinsu dan kasar ta Thailan ne, kuma ba za a biya su kudi ba.

Sabuwar dokar ta biyo bayan cece-kucen da ya biyo bayan wani karamin yaro mai suna Gammy wanda aka haifa a watan Agustan bara ne.

Wasu ma'aurata 'yan Australia ne suka biya mahaifiyar yaron, Pattaramon don ta dauki ciki ta haifa masu jariri, amma sai suka dauki 'yar uwar tagwaitakarsa saboda shi gala-gala ne wato yana da cutar da ake kira DOWN SYNDROME a turance.

Haka kuma an gano wani dan kasar Japan da mata daban-daban suka haifa masa 'ya'ya 16.

Wani dan majalisar kasar na ganin sabuwar dokar za ta hana a maida kasar ta zama wajen samar da 'ya'ya ga duniya ba.

Sai dai a kasar da ba a cika bin doka ba, yawan kudin da ake biya zai iya sanya wa mata talakawa kwadayin zama iyayen sojan gona ga 'yan kasashen waje ta haramtacciyar hanya.