Duk wanda ya ci zabe za a ba shi- Sambo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An dage zaben Nigeria zuwa ranar 28 ga watan Maris

Mataimakin Shugaban Nigeria, Alhaji Namadi Sambo ya fadawa BBC cewa za a rantsar da duk wanda ya lashe zaben kasar ranar 29 ga watan Mayu.

Mataimakin Shugaban Kasar ya ce burinsu shi ne demokradiya ta kara kafuwa a Nigeria sannan a kuma yi sahihin zabe.

Alhaji Namadi Sambo ya kuma ce gwamnatinsu ta PDP ta taka rawar gani a bangaren samar da hasken wutar lantarki da shimfida titunan jirgin kasa da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

A watan gobe ne dai za a gudanar da babban zaben kasar.

Shugaba Goodluck Jonathan mai ci na Jam'iyyar PDP mai mulkin zai fafata da dan takarar Shugabancin kasar karkashin inuwar jam'iyyar adawa ta APC, janar Muhammadu Buhari mai ritaya.

Masu sharhin siyasa a Nigeria na ganin cewa wannan shi ne zai kasance zabe mafi zafi da za'a fafata a kasar.