'Yan Boko Haram sun kai hari a Nijer

Hakkin mallakar hoto

Mayakan Boko Haram sun kai hari a wani tsibiri da ke kusa da Tabki Chadi, a bangaren Jamhuriyar Nijer.

Rahotanni sun ce mayakan sun kai harin ne ranar Juma'a da daddare a garin Karamga, inda wasu 'yan gudun hijira daga Najeriya suka samu mafaka.

Majiyoyin tsaro sun ce an fafata sosai tsakanin 'yan Boko Haram da jami'an tsaron Nijer a harin, wanda suka ce ya janyo asarar rayuka.

An ce dakarun kasar Chadi ma sun kai dauki a ranar Asabar kafin ayi nasarar murkushe 'yan Boko Haram din.

A waje daya kuma Shugaba Mahammadou Issofou na Nijer din zai fara wata ziyara a Diffa bayan matsalar hare-haren mayakan Boko Haram da ta addabi yankin.

Karin bayani