Venezuela: An zargi magajin-gari da shirya juyin mulki

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An yi awon gaba da magajin garin babban birnin Caracas

Masu gabatar da kara a Venezuela sunce su na wani shiri na tuhumar magajin garin Caracas, babban birnin kasar, bisa hannu a wani shiri na hanbarar da gwamnati.

An tsare Antonio Ledezma wanda dan siyasa ne na bangaren 'yan adawa a ranar Alhamis, bayan wasu mutane sanye da kakin soji sun kutsa kai cikin ofishinsa ta karfin tsiya.

Shugaban Kasar Venezuelan Nicolas Maduro ya zargi Amurka da hannu a shirin hanbarar da gwamnatinsa.

Sai dai Wani mai magana da yawun fadar White House ya ce babu gaskiya a zarge zargen.