Mata 3 a Burtaniya sun je shiga kungiyar IS

Image caption 'Yan matan 3 sun bar gidajen iyayensu domin shiga kungiyar IS a Syria

Iyayen wasu 'yan mata 3 da ake fargabar sun yi balaguro zuwa Syria domin shiga cikin kungiyar IS sun roki 'ya'yan nasu da su yi hakuri su koma gida.

Anyi wa 'yan matan wadanda suka tafi daga Landon gani na karshe a ranar Talata, lokacin da suka hau jirgi zuwa Istanbul.

'Yan matan, Kadiza Sultana mai shekaru 17, da kuma Shamima Begum da Amira Abase masu shekaru 15, kawayen juna ne.

Kasar Turkiya ta zamo babbar hanya ga jama'a ta shiga cikin Syria.

Kwararru a fannin yaki da ta'addanci sun yi kiyasin cewa kimanin mata 50 ne suka yi balaguro daga Burtaniya zuwa Syria somin shiga cikin mayakan kungiyar ta IS, wadda ta mamaye muhimman wurare a Iraki da Syria.