Ta'addanci: Ana bukatar gyara a manhaja

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Sheikh Ahmed Al-Tayib ya ce gurguwar fahimtar addinin musulunci yasa wasu ke daukan tsatstsaurar akida

Limamin Jami'ar Al-Ahzar ta kasar Masar ya yi kiran a yi garanbawul a manhajar koyarwar addinin musulunci domin yaki da tsatstsaurar akidar kishin musulunci a kasashen musulmai.

Sheikh Ahmed Al-Tayib ya shaida wa taron yaki da ta'addaci cewa a Makka cewa rashin fahimtar koyarwar Alkur'ani da tarihin Annabi Muhammad (SAW) sun taimaka wajen samun rashin daidaito a tsakanin musulumai.

An shirya taron ne kan yadda addinin musuluncin zai magance matsalar masu fake wa da shi suna aikata ta'addanci.

Sheikh Al-Tayib ya ce gurguwar fahimta da wasu su kayi wa Alkur'ani mai tsarki da kuma sunnar Annabi Mohammad (SAW) sun dasa tsatstsaurar akida ta kishin islama a zukatan wasu musulmai.

Sarkin Salman bin Abdul'aziz na kasar Saudi Arabiya ya ce tsatstsaurar akida ta kishin islama tana barazana ga musulmai da kuma bata sunan su a duniya.