Austria za ta sabunta doka don Musulmi

Sebastian Kurz Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ministan Hadin Kan Kasa Sebastian Kurz ya ce Austria na son Musuluncin da ya dace da ita

Majalisar dokokin Austria ta amince da yin wani garambawul mai cike da ce-ce-ku-ce kan dokar kasar da ta shafi addinin Musulunci wacce ta kai shekaru 100.

Sabuwar dokar za ta bai wa Musulmin kasar damar daukar hutu a ranakun bukukuwan addini ba tare da an ladabtar da su ba, sannan kuma a rika karantar da su addini a cibiyoyin hukuma irin su gidan yari da asibitoci.

Sai dai dokar za ta kuma takaita taimakon kudin da masallatai ke samu daga kasashen waje, ta kuma jaddada cewa dokar kasa na sama da akidu na addini.

Amma shugabannin Musulmi sun nuna cewa sabuwar dokar alama ce ta rashin yarda da Musulmai, sannan kuma ta gaza wajen daidaita su da sauran 'yan kasa.

Wadansu daga cikinsu ma na shirin kalubalantar dokar a gaban kotun tsarin mulki.

Sebastian Kurz, ministan harkokin wajen Austria ya ce, "Wannan doka ba ta nufin cin zarafin kowa. Kasar Austria na son samar da wani nau'i ne na addinin "Musulunci wanda ya dace da dabi'un mutanen kasar kawai".