BBC ta zabi kamfanonin da za su watsa shirye-shiryenta

Image caption BBC na kokarin kai wa ga wani bangare na matasa a Afrika

BBC ta zabi wasu kamfanoni biyu na kasar Kenya wadanda za su dunga watsa shirye-shiryenta ta hanyar shafukan zumunta na zamani.

An zabi Go Sheng Services da kuma Ongair daga cikin kamfanoni 13 daga kasashen Afrika da kuma Amurka wadanda suka shiga takarar.

A farkon wannan watanne BBC ta shirya wani taro mai suna "hackathon" a birnin Nairobi na Kenya domin tattance wadanda suka nuna fasaha wajen ba da labarai ga al'umma.

Za a samar musu da kudade domin cimma abin da suka sa a gaba a cikin watanni shida.

Dmitry Shishkin editan BBC a bangaren shafukan zumunta na zamani ya ce "Na yi matukar murnar sanar da wadannan kamfanonin wadanda za su samar da labarai ta wasu sabbin hanyoyi."

Kamfanin Go Sheng Services zai dunga samar da labaran BBC ne a harshen Sheng na Kenya domin matasa.

A bangaren kamfanin Ongair kuwa, za su dunga bukatun matasa ne domin tattance irin labaran da za su aika musu.