"Faduwar Naira ba zata shafi aikin gwamnati ba." Amb. Yuguda

takardar kudin Najeriya, Naira
Image caption takardar kudin Najeriya, Naira

Minista a ma'aikatar kudi ta Najeriya, Ambasada Bashir Yuguda ya ce idan da Nijeriya ta dogara ne kacokan kan man fetur wajen samun kudin shiga, da an shiga cikin wani mawuyacin hali.

A cikin wata hira da sashen Hausa na BBC kan matsalar faduwar darajar Naira, Ambasada Yuguda ya ce, " Abin da ke shigo aljihun Nijeriya, ba daga mai ba ne kawai, da daga mai ne kawai, yadda farashin man yayi kasa gaba daya, da yanzu albashi ma kusan sai an gagara biyansa.

Ministan ya ce suna daukar matakai na tabbatar da farfado da darajar Naira.

A tsakiyar wannan watan ne dai takardar kudin ta yi faduwar ba ta taba yi ba a kan dalar Amurka sakamakon faduwar farashin mai da kuma bayar da sanarwar dage manyan zabukan kasar da aka shirya yi ranar 14 ga wannan watan.