An yanke wa dan Masar hukuncin dauri a kurkuku

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Alaa Abdel Fattah zai shafe shekaru biyar a gidan yari

Wata kotu a Masar ta yanke hukuncin daurin shekaru biyar kan wani dan gwagwarmayar siyasa da ya taka rawa lokacin juyin juya halin da aka yi a kasar.

An yanke wa Alaa Abdel Fattah hukuncin ne saboda karya dokar da ta hana mutane shiga duk wata zanga-zanga ba tare da izinin gwamnati ba.

Kakakin jam'iyyar Liberal constitution, Khaled Dawoud, ya yi Allah-wa dai da hukuncin:

Ya ce "Wannan tsantsar zalinci ne da kuma kokarin ci gaba da muzgunawa matasa tare da da kushe hobbasarsu. Babu wa ta doka da wadannan matasan su ka karya tunda zangar-zangar da su ka gabatar ta lumana ce."

A zaman farko na shari'ar, hukuncin shekaru 15 aka yanke ma sa, amma ya sami sassauci bayan da ya daukaka kara.