Dalibai a Ghana sun yi zanga-zanga kan hijabi

Image caption Gwamnatin Ghana ta hana tilastawa wani wajen yin wani addini

A kasar Ghana dalibai Musulmi na makarantun Sakandare a wasu sassan kasar sun yi zanga-zanga don nuna bacin ransu game da hana su sanya hijabi

Haka kuma daliban sun yi zargin cewa hukumomin makarantun suna hana matan da ke makarantunsu gudanar da addininsu.

A karshen makon da ya gabata ne wasu shugabannin Musulmin kasar suka yi wata ganawa da hukumar tabbatar da zaman lafiyar kasar kan wannan lamari.

Hukumar dai ta ce lamarin abu ne wanda zai kawo cikas ga zaman lafiya.

Haka zalika hukumar zata kafa kwamiti wanda zai binciki korafe-korafen da shugabannin Musulmin suka gabatar.

Bayan nan ne kuma za a kira shugabannin addinai daban-daban a sasanta yadda za a bai wa kowa hakkinsa na dan kasa.