Tashin bam: Ana ci gaba da harka a Kano

Daya daga cikin mutanen da suka yi rauni a harin
Image caption Mutane 26 ne ke karbar magani a asibiti

A birnin Kano na arewacin Nigeria, komai ya koma daidai a tsohuwar tashar Kano Line, kwana biyu bayan wani harin kunar-bakin-wake ya yi sanadiyyar asarar rayuka.

Ranar Talata ne dai aka kai harin na kunar-bakin-wake a tashar, inda mutuwar mutane 12 suka rasa rayukansu, wasu 26 kuma ke ci gaba da karbar magani a asibiti.

Wadansu daga cikin direbobin da wakilin BBC Yusuf Ibrahim Yakasai ya tattauna da su a tashar sun ce ganin matakan tsaron da aka dauka ya karfafa musu gwiwar ci gaba da harkokinsu kamar babu abin da ya faru.

"Muna ci gaba da harkokinmu [saboda] yadda aka dauki matakan tsaro na kare wannan tasha—kare fasinjoji da dunkiyoyinsu, da direbobi da fasinjojinsu", inji daya daga cikin direbobinsu.

Su ma fasinjoji sun ci gaba da zuwa tashar don shiga mota, kuma daya daga cikinsu ya bayyana cewa: "...Ba wata fargaba da ke damuna—ina da kwarin gwiwa cewa duk abin da Allah Ya kaddara ma ba yadda za ka yi".

A yanzu dai babu mai shiga tashar sai an bincike jikinsa da kayansa. Masu shiga tashar kuma ba sa nuna damuwa. Hasali ma daya daga cikin fasinjoji cewa ta yi: "Ba damuwa, wannan mun saba da shi..."