Mutane 12 bam ya kashe a Kano —'Yan sanda

Image caption Wani da harin 'yan Boko Haram ya rutsa da shi a watannin baya.

'Yan sanda a birnin Kano na arewacin Najeriya sun ce mutane 12 ne suka rasa rayukansu a harin bom din da aka kai a tsohuwar tashar motar Kano Line, wacce aka fi sani da Karota Motorpark.

Kakakin rundunar, ASP Magaji Musa Majiya, ya ce 'yan kunar-bakin-wake biyu ne, wadanda suka je tashar a mota kirar Sharon mai dauke da mutane shida, suka tashi bom din.

'Yan kunar bakin waken na cikin mutane goma sha-biyun da suka rasa rayukansu.

Wani wanda ya ke tashar lokacin da lamarin ya faru ya ce ya ga sassan jikin dan-Adam, sannan kuma wadansu gawarwakin sun yi mummunar konewa.

Akalla mutane goma sha uku ne suka rasa rayukansu a wani harin mai kama da wannan a wata tashar mota a garin Potiskum na Jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai hare-haren, amma kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare irin wannan, ciki har da wanda aka kai wata tashar motar a unguwar Sabon Gari, a birnin na Kano.