Mawuyaci ne mu shiga yaki da Ukraine- Putin

Hakkin mallakar hoto n
Image caption Mista Putin yana fuskantar matsin lamba a game da Ukraine

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce abune mawuyaci kasarsa ta shiga yaki da Ukraine.

A wata fira ta talabijin, Mista Putin ya nuna goyon bayansa ga yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a Minsk, wadda ya bayyana a matsayin hanyar samun zaman lafiya a gabashin Ukraine.

Shugaba Putin ya musanta zargin da Ukraine ta ke yi a kan cewa sojojin Rasha suna shiga cikin fadan da ake yi a yankin.

Ya ce gwamnatin Ukraine tana fakewa ne da wannan zargi domin abin kunya ne a ce 'yan tawaye suna yin galaba akan sojojinta.

Ya kuma dage a kan bakarsa cewa Rasha ba zata mayarwa Ukraine yankin Cremea da ta mamaye bara ba.