Taro kan hanyoyin sada zumunta a Nigeria

Hakkin mallakar hoto GETTY
Image caption Hanyoyin sada zumunta na intanet na taka rawa a rayuwar al'umma

A Najeriya, ranar Litinin ne aka bude wani taron shekara-shekara a kan yadda ake amfani da hanyoyin sada zumunta da muhawara wajen bunkasa ci gaban al'umma.

Taron na bana zai duba yadda ake yin amfani da wayoyin salula wajen kawo sauyi a rayuwar dan-Adam.

Mahalarta taron za su kuma duba irin rawar da hanyoyin sada zumunta da muhawara ke takawa musamman a zaben Najeriya na shekarar 2015.

Kazalika mahalarta taron na duba irin tasirin wadannan hanyoyi wajen hada kan al'ummar duniya da tabbatar da mulkin dimokradiyya.

A cewarsu, ya zama wajibi a sanya idanu a kan wadannan kafofi, ganin irin tasirin da suke yi wajen wanzar da mulki na gari.

A kasashe da dama dai ana yin amfani da wadannan hanyoyi wajen tilastawa gwamnatoci yin abubuwan da jama'a ke so.

A Najeriya, an yi amfani da wadannan hanyoyi a shekarar 2011 domin yin zanga-zargar da ta tilasta wa gwamnati sauya matsayinta bayan karin kudin man fetur da ta yi.