'Amfani da sirinji mara kyau na yada cututtuka'

Hakkin mallakar hoto EyeWire
Image caption Matsalar amafani da sirinji guda ga mutane da yawa ta fi kamari a kauyuka

Hukumar lafiya ta duniya ta kaddamar da wani shiri na rage yaduwar cututtuka ta hanyar amfani da sirinji marasa kyau.

Miliyoyin mutane ne ke kamuwa da cutar HIV da ciwon suga sakamakon yi musu allura da sirinji mara kyau a duk shekara.

A wani kauye a Cambodia fiye da mutane 270 ne suka kamu da cutar HIV saboda wani wanda ba jami'in lafiya ba ne ya yi musu amfani da sirinji daya, hakan kuma ya taimaka wajen yada cutar ta HIV.

Hukumar ta bukaci a fara amfani da sabon matakin yin amfani da sirinji daya ga mutum guda.

Abin da hukumar ke fatan zai zamo matakin da ake amfani da shi nan da shekarar 2020.