'Yan matan Biritaniya sun shiga Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan matan sun shiga jirgi daga London zuwa Istanbul

'Yan sanda a Biritaniya sun ce sun yi imanin cewa 'yan matan nan uku da suka yi balaguro zuwa Turkiya daga London a makon da ya gabata, a yanzu sun shiga kasar Syria.

Ana fargabar cewa suna da niyyar hade wa da mayakan kungiyar IS ne.

Wasu majiyoyi a Syria sun shaida wa BBC cewa, masu fasakaurin mutane sun tsallakar da 'yan matan zuwa garin Kilis da ke kan iyaka kwanaki hudu ko biyar da suka wuce.

Daliban na makarantar sakandare ta Bethnal Green su ne; Shamima Begum da Amira Abase, 'yan shekaru 15 da Kadiza Sultana 'yar shekaru 16, a ranar 17 ga watan Fabarairu suka shiga jirgin sama zuwa Istanbul.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da iyayen yaran suka yi kira garesu su dawo gida.