Boko Haram: An sanya dokar hana kai kifi Diffa

Hakkin mallakar hoto alberdeen
Image caption An tare motocin kifi dayawa a Diffa

A jamhuriyar Nijar, hukumomin jihar Diffa sun sanya dokar hana shiga da kifi daga Bosso zuwa Maiduguri da wasu sassa na Nigeria.

Hukumomin sun ce sun dauki matakin ne domin hana kai wa 'yan Boko Haram abinci da sauran kayayyakin masarufi, da ake sayo musu da kudaden kifin.

Wata majiya ta soji ta ce bincike ya nuna cewa direbobin motocin dakon kaya suna kai kifin 'yan Boko Haram kasuwa, inda suke saya musu shinkafa da madara da mai da sauransu da kudin kifin.

Hukumomin Diffa sun tilasta wa direbobin rantsuwa da Alkur'ani a kan kifin da suka yi dakon shi ba na Boko Haram ba ne, kafin a bari su wuce da shi.

Jihar Diffa ta yi fama da hare-haren Boko Haram a 'yan kawanakin nan.