An amince da kara ceto tattalin arzikin Girka

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Hukumar tarayyar Turai ta ce shawarar Girka ta cancanci zama mafarin tattaunawa

Kasashen da ke amfani da kudin euro sun amince da a kara ceto tattalin arzikin kasar Girka bayan sun duba shirinta na garambawul.

Hakan ya biyo bayan tattaunawar da ministoci na kasashen da ke amfani da kudin euro suka yi a ranar Talata.

Tun da fari dai shugaban kungiyar, Jeroen Dijsselbloem, ya ce Girka da gaske ta ke yi, amma abubuwa ba za su kasance da sauki ba.

Ya ce "Girka ta gabatar da wadansu matakan sauye-sauye a ranar Litinin, sai dai ya zo a kurarren lokaci amma kuma zai iya yin tasiri. Don haka wannan hukuma da kuma hukumar ba da lamuni zasu duba wadannan jerin sauye-sauye don ganin irin abin da su ka kunsa."

Girka dai na son ta saukaka shirin tsuke bakin aljihunta, amma kuma sai ta yi la'akari da kasafin kudin kasar.

Ta ce za ta yi hakan ta hanyar samar da biliyoyin kudin euro na kudaden shiga ta hanyar karbar haraji da shawo kan matsalar kin biyan haraji da kuma cin hanci da rashawa .

Da ace ba a amince da bukatun Girkar ba, da an tilasta wa kasar ta daina amfani da kudin euro.