'Yan IS sun sace 'Kiristoci 70' a Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mayakan kungiyar IS na fada da gwamnatin Iraki da na Syria

Mayakan kungiyar IS sun sace mutane da dama a kyauyukan kiristoci da ake arewa maso gabashin Syria.

Wata kungiyar kare hakkin 'yan Syria ta ce an sace akalla maza da mata da kuma kananan yara 70 a garin Tal Tamr lokacin da 'yan kungiyar IS suka kai samame da sanyin asuba.

Wasu daga cikin kiristocin sun tsere inda suka gudu zuwa birnin Hassakeh a yankin gabashin kasar da ke karkashin ikon Kurdawa.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da mayakan Kurdawa da dakarun Amurka ke nausawa zuwa yankunan da ke karkashin ikon kungiyar IS.

Lardin Hassakeh na da mahimmanci a yakin da ake yi, saboda yana kan iyaka ne da Turkiya da kuma yankunan Iraki da ke karkashin ikon kungiyar IS.