Bam ya fashe a tashar motar 'Kano Line'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Rahotanni daga Kano na cewa bam ya fashe a tashar motar da ake kira 'Kano Line' a cikin birnin.

Lamarin wanda ya faru da rana lokacin hada-hadar jama'a, ya janyo mutuwar mutane da jikkatar wasu da dama.

Kawo yanzu babu cikakkun bayanai a kan adadin wadanda lamarin ya rutsa da su, sai dai shaidu sun ce sun ga gawawwaki kwance a kasa.