Zamu kasa,mu tsare a ranar zabe - Kwankwaso

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gwamna Rabiu Kwankwaso

Gwamnan jihar Kano kuma dan jam'iyyar adawa ta APC, Dr. Rabi'u Musa kwankwaso ya ce a ranar zabe babu wanda zai yi musu barazana, domin za su kare akwatunansu.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC in da ya ce " Kuma ranar zabe ka san kamar yadda ake fada soja malamin kansa, mu 'yan siyasa mu ne soja malamin kanmu, kowa ya zo soja ne muma tare akwatunanmu za mu yi babu wanda zai yi mana wata barazana."

Haka kuma tsoshon ministan tsaron na Najeriya ya ce yana ganin da wuya a yi amfani da sojoji wajen magudin zabe domin " Idan an sa su ina ganin ba za su dauki umarni ba tun da suna da tsarin yadda suke aiki."

Inda ya kara da cewa "A sani na dai sojojin nan manyan kawai shugaban kasa yake da su, amma duk wani soja ta kansa yake, so yake a samu zaman lafiya a Najeriya."

Abin da yasa ya bayyana kwarin gwiwar cewa idan zabe ya zo komai zai tafi yadda ya kamata.

'Dage zabe'

Gwamnan na Kano ya ce gwamnati tay amfani da sojoji ne wajen dage zabukan kasar, amma sosoji basu da wata harka da siyasa a kasar.

Inda ya kara da cewa mutuncin shugabannin Najeriyar ya zube saboda magana biyu.

"Shugaba abin da ka fada a daki ka fito waje ka fada, abin da ka fada a waje in ka zo daki ma ka fade ."

"Wadannan mutanen duk abokanmu ne, mun san makaryaci a ciki, mun san wanda zai fadi gaskiya a ciki, mun san yanayin da zai zo ya fada da sauransu." In ji gwamnan.

'Ficewar Obasanjo'

Haka kuma gwamna Kwankwaso ya yi tsokaci game da ficewar tsohon shugaban kasar, Cif Olusegun Obasanjo daga jam'iyyar PDP mai mulki.

Inda ya ce Obasanjo ya hango abin da ya sa suka fice daga PDP kuma, ficewarsa ta tabbatar da cewa abin da suka yi daidai ne.