Dan kunar bakin wake ya kai hari a Potiskum

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai hari, ko da yake ya yi kama da na Boko Haram

Rahotanni daga garin Potiskum na Jihar Yobe a Najeriya na cewa wani dan kunar bakin wake ya kai hari a wata tashar mota.

Lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 18, yayin da wasu kuma suka jikkata.

Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa wani fasinja ne da ya fara shiga mota kirar bas da leda a Tashar Danborno, inda ya tashi bam din da yake dauke da shi bayan motar ta cika.

Wanda lamarin ya faru a gabansa ya kara da cewa babu wanda ya tsira a motar mai daukar mutane kusan 18, wanda ta kone kurmus.

Sai dai har yanzu hukumomi ba su tabbatar da faruwar lamarin ba.

A baya-bayan nan dai garin na Potiskum ya fuskanci hare-haren kunar bakin wake da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.