Ebola: Saliyo ta ce ta koyi babban darasi

Image caption Saliyo za ta soma aikin gina tattalin arzikinta ba sai an kauda annobar ebola ba

Ministan harkokin wajen Saliyo ya ce ba za a jira aikin sake gina tattalin arzikin kasar ba, har sai lokacin da annobar Ebola ta kau.

Samura Kamara ya fadawa BBC cewa bunkasa ci gaba, zai taimaka wajen samun kudaden da ake bukata domin samar da kayayyakin da ake bukata a bangaren kiwon lafiya.

Ya ce 'babban darasin da aka koya game da annobar Ebola shine Saliyo na bukatar ta kara zuba jari akan tsarin kiwon lafiyarta'.

Ministan na magana ne a London gabanin wani babban Taro da zai tattauna yadda za'a sake gina tattalin arzikin Saliyon--- wanda har ya zuwa lokacin da Ebola ta shiga ke farfadowa daga yakin basasar kasar