Kotu ta ce Palasdinawa su biya Amurkawa diyya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kotu ta ce Palasdinawa su biya Amurkawa dala miliyan 200

Wata Kotu a Amurka ta bada umarnin cewa kungiyar 'yan tarda al'ummar Palasdinawa ta PLO da kuma hukumar Palasdinawa su biya diyya ga wasu Amurkawa da hare- hare ya shafa a birnin Qudus fiye da shekaru goma da suka gabata.

Alkalan a New York sunce Palasdinawan zasu biya fiye da dala miliyan 200 a matsayin diyyar harbe- harbe shida da kuma tayarda bom tsakanin shekarar 2002 zuwa 2004, wanda mutane 33 suka mutu sannan fiye da dari suka samu raunuka.

An dora alhakin hare -haren akan rundunar al-Aqsa da kuma Hamas, amma iyalan Amurkawan wadanda hare- haren ya shafa sun bukaci a tuhumi kungiyar ta PLO da kuma hukumar Palasdinawa.

Dukkanin bangarorin biyu dai ana tsammanin zasu daukaka kara