Ana ci gaba da cafke 'yan adawa a Venezuela

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban kasar na zargin 'yan adawa da kokarin hanbarar da shi

Jam'iyyun adawa a Venezuela sun yi allawadai da tsare shugabanninsu a 'yan kwanakin nan, sannan kuma sun yi watsi da zarge zargen gwamnatin kasar cewa suna shirya wani juyin mulki.

Babbar gammayar jam'iyyun adawa tace wadanda suke da sojoji da makamai sune kadai zasu iya shirya wani juyin mulki, kuma gwamnati ita ke da cikakken iko da sojojin kasar.

Shugaba Nicolas Maduro ya sha zargin abokan hamayyarsa da shirya makarkashiya tare da Kasar Amurka domin hanbarar da shi.

Masu suka sun ce yana kokarin ya kauda hankalin 'yan kasar ne daga rikicin Tattalin arzikin da kasar ta samu kanta ciki