Sojin Congo sun kai hari kan 'yan tawayen

Sojojin Congo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojoji sun kaddamar da hare-hare ta sama domin tarwatsa 'yan tawayen FDLR.

Dakarun sojin jamhuriyar dimukradiyyar Congo sun kaddamar da hare-hare ta sama akan 'yan tawayen Hutu na Rwanda da ke kasar, jami'an gwamnati sun ce an kai hari na farko da aka sanar za a kai tun a watan da ya wuce domin tarwatsa 'yan tawayen.

Kungiyar 'yan tawayen FDLR, wadanda suka hada da tsaffin sojoji da mayakan sa kai na kabilar Hutu wadanda suke da alhakin kisan kiyashin da ya faru a a kasar Rwanda a shekaarr 1994, sun shafe kusan shekaru 20 su na yaki a jamhuriyar Dimukradiyyar Congo.

Kwamandan da ya jagoranci Harin da aka kai a jiya talata ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa, sun kaddamar da shi ne a kudancin Lardin Kivu, kusa da tsaunin garin Uvira mai nisan kilomita 10 da iyakar kasar da Burundi.

Shi ma wani sojan Congo ya ce harin da aka dade ana shirya yadda za kai shi, ya mamaye kusan dukkan manyan wuraren da 'yan tawayen FDLR suke zama a tsaunin Moyen da ke Mulenge. Haka kuma maimagana da yawun dakarun sojin Congo Leon Kasonga ya sanar da cewar rundunar su ta yi nasarar kahe uku daga cikin mayakan 'yan tawayen.

Ya yin da 'yan tawayen na FDLR suke a kudancin garin na Kivu, akwai rahotannin da ke cewa akalla kimanin mayakan yan tawayen 1400 ne suke kaddamar da hare-harensu a rewacin lardin na Kivu.

Rundunar MDD dai ta janye tayin da ta yi ne na taimakawa bayan gwamnatin ta tura wasu janar-janar biyu a wannan runduna - alhali kuma ana zarginsu da hannu a laifukka na cin zarafin bil-adama.